HUDUBAR JUMA’A: An Gudanar Da Addu’O’I Na Musamman Ga Gwamna Uba Sani, Hon. Sani Rabi’u Bako, Kaduna, Da Najeriya   

Daga Sanee Yarima – Kaduna 

An danganta ranshin zaman lafiya da Kasarnan ke ciki da rushin kulada Marayu da Miskinai, tare da jawo hankalin Musulmi dasu maida hankali a bangaren.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Jama’atu dake kan Titin Nupe dake Jahar Kaduna, Imam Muhammad Kamir bayyana hakan a Hudubar sa na Ranar Juma’a 8 ga watan Agusta,  2025. 

Kaman yadda aka sani, Maraya shine wanda Mahaifin sa ko nata ya rasu, tohh amma Marayan dake bukatan taimako shine wanda ba yadda zaiyi karatu ko wata sana’a sabo da karacin shekaru.

Imam Muhammad Kamir, yace akwai bukatan Al’umman Musulmi dasu kara kaimi wajen taimaka wa Marayu, harma da Miskinai domin samun yardan Ubangiji, da kuma zaman lafiya a Kasa.

“Mun lura yanzu a gidaje da yawa ana wulakanta Marayu, adon haka Hudubar mu ta yau ta jawo hankalin Musulmi da mu rinka taimaka musu, da Miskinai, dama duk wadan da suka chanchanci taimakawa. Idan muna haka, toh ALLAH zai kawo mana zaman lafiya da bunkasan arziki a kasa baki daya,” Imam Kamir ya jaddada.

Babban Limamin Masallacin Juma’an na Jama’atu, ya yace Manzon ALLAH S.A.W yana cewa “Mafi Alkhairin gida, shine gadan da ake kyautata wa Marayu, sannan kuma mafi sharri daga cikin gidajen Musulmi shine gidan da ake Kuntata ma Marayu.”

Imam Muhammad Kamir ya kara da cewa, kyautata wa Marayu na kunshe da lada mai tsoka daga wajen ALLAH S.W.A. 

Kazalika, jim kadan bayan kammala Sallan Juma’an mai raka’o’i biyu, Imam,Imam Muhammad Kamir, Mallam Umar Bin Umar da kuma Mallam Kabiru Babasidi sun gudanar da addu’o’i na musamman ga Shugabanni, Jahar Kaduna, da Najeriya baki daya.

Malaman Addinin Musuluncin, sun kuma shawarci Alhaji Sani Rabi’u Bako da yayi amfani da Mukamin da Gwamna Uba Sani ya bashi wajen samun Aljannah, dare yi masa fatan alkhairi. 

A kwana kinnan ne, Gwamna Uba Sani na Jahar Kaduna, ya nada Hon. Sani Rabi’u Bako a matsayin Shugaban Hukumar Lura da Al’amuran Kasafin Kudi na Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *