Daga Sani Yarima
Dalibai biyu wanda akayi garkuwa dasu domin neman kudin fansa dake Jami’ar Tarayya dake Wukari a jihar Taraba sun kubuta daga hannun wadan da suka sace su.
Jami’ar harkan yada labarai da tsatsare na Jami’ar, Ashu Agya ta shedawa SAHEL REPORTERS cewa an sako daliban ne a daren jiya Alhamis 11/4/2024 a wani yanki dake karamar hukumar ta Wukari.
Agya ta kara da cewa an bada naira dubu dari bakwai (N700,000) a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutanen, sabanin naira miliyan hamsin (N50m) da suka nema a farko.
Majiyar tamu ta kuma tabbatar da cewa daliban na cikin koshin lafiya.
Idan ba’a manta ba, daliban guda biyu, anyi garkuwa dasu ne a wani dakin saida abinci dake cikin Jami’ar a ranar Litini 1/4/2024 kimanin kwanaki goma sha daya kenan.