News  

TSADAN RAYUWA: A Dena Luwadi, Zina, Shan Giya, Chuta Da Zalunci- Ustaz Hamman Adama 

Daga Sani Yarima 

An gargadi al’umman Musulmi dasu guji aikata luwadi, zina, shan giya, ha’inci, da duk sauran ayyukan sabon Allah.

Limamin Masallacin Juma’a na Muslim Council dake Jalingo, Ustaz Bashir Hamman Adama shine yayi gargadin a Huduban sa na Sallan Juma’a daya gudanar a yau 12/4/2024.

Ya karanto ayoyin Alqur’ani mai girma da Hadisan Manzon ALLAH (SAW) inda yace duk mai sabon Allah ya jira sakamako na zuwa, domin ba’a taba sabawa Allah a zauna lafiya kuma a gama da duniya lafiya, ba tare da an tuba ba. 

Hamman Adama ya lura da cewa, rashin gaskiya, cin amana, yaudara da ha’inci sunyi wa al’umma katutu a zamanin yanzu, adon haka yayi kira ga Musulmi dasu gyara ayyukan su, su tuba su koma ga Allah.

Ya kara jaddada bukatar Dake akwai na “Jama’a su guji son duniya fiye da jin tsoron Allah, su dena shan giya, zina, karya, da dukkan sauran ayyukan fasikanci a doron kasa domin samun tsira ranan gobe kiyama.

“A fifita jin tsoron Allah fiye da wani shugaba ko mai arziki. Kawai za kaga mutane sunfi jin tsoron Gwamna, ko wani Dan Majalisa, ko Mai kudi fiye da maganan Allah. Tohh wallahi mu tuba mu koma ga Allah.

“A lokacin watan Ramadan daya gabata, Malamai sun fassara ayoyin Alqur’ani a ko ina, toh amma saboda sakaci al’umma da damana basu daukan darasin sabo da son duniya.

“Rashin tawakkali da tsoron Allah shi yasa Jama’a ke cikin wahala,” inji Ustaz Hamman Adama.

Ya kuma yi kira ga masu hanu da shuni dasu rinka ciyar da marasa galihu, marasa lafiya, Marayu, gyara Masallatai, yana mai cewa bawai lalle sai masu kudi ba, idan har Mutum nada koda naira dari (N100) ne, toh zai iya taimakawa wani ko masallaci da nera hamsin.

A wata ayar Al’qur’ani Mai Girma daya jawo “ALLAH (SWA) ya bayyana masu aikata wadannan abubuwan alkharin da cewa sune mumunai na gaskiya Kuma ALLAH yayi alkawarin yin gafara gare su a ranan kiyama.

Malamin addinin Musuluncin, Ustaz Bashir Hamman Adama ya kara jaddada bukatar dake akwai na al’umman Musulmi dasu tuba zuwa ga Ubangiji, domin acewar sa alamun ‘”Tashin Alkiyama yazo”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *