Daga Sani Adamu Hassan
Shugaba ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce bayan janye tallafin daka yi, kasar ta samu nasarar adana Naira Tiriliyan biyu a asusun kasa.
Bisa cewarsa, wannan sauye-sauyen ya samar da sakamako mai kyau, a don haka hakuri da juriya ake bukata.
Shugaban ya fadi hakan ne a yayinda yake jawabi wa ƴan Nigeria kan halinda ƙasar ke ciki.
Inda ya kara da cewa, a matsayin sa na shugaban Nigeria zai cigaba da jajircewa wajen ganin ya samarda shuagabanci na kwarai.