Hausa  

Yan Ta’adda 4 Sun Shiga Koman Dakarun 6 Brigade Tare Da Makaman Su A Jihar Taraba

Daga Wakilin Mu 

Dakarun 6 Brigade na Rundunar Sojin Najeriya/Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) na ci gaba da samun nasarori a yaki da ta’addanci da aikata laifuka a Jihar Taraba. 

Kyaftin Olubodunde Oni, Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na 6 Brigade, Rundunar Sojin Najeriya, shine ya sanar da hakan a wata takarda daya baiwa manema labarai a rabar Laraba 7 ga watan Mayu, 2025.

A wani samame da suka gudanar a ranar 7 ga watan Mayu, 2025, takardan take, dakarun sun kama mutane huɗu da ake zargin ‘yan ta’adda ne tare da kwato makamai da alburusai a yankin Tau da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola.

Aikin ya biyo bayan samun kiran gaggawa ne dangane da motsin wasu mutane dauke da makamai zuwa yankin.

Takardan ta kara da cewa, “Dakarun sun yi gaggawar kai dauki tare da tashi da dabaru zuwa wurin, inda hakan ya kai ga kama mutane huɗun, yayin da uku daga cikinsu na rike da makamai.

“Kayan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da: bindigogi nau’in pump-action guda 2, bindiga da aka ƙera a gida guda 1, adduna guda 3, alburusai guda 42, wayoyin hannu guda 4 da katin shaidar Dan ƙasa guda 1.

“Binciken farko ya nuna cewa ana zargin wani mai suna Alhaji Ardo Sani da kiran wadannan mutanen zuwa yankin, kuma ana ci gaba da bincike kan rawar da ya taka a lamarin.

“Kwamandan 6 Brigade/Sector 3 OPWS, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa dakarun bisa gaggawa da ƙwarewar da suka nuna yayin aikin. 

Birgediya Uwa, ya kuma sake jaddada kudirin Rundunar Sojin Najeriya wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a cikin Jihar Taraba da kewaye.

Kazalika, an shawarci al’ummar gari da su ci gaba da ba da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa ayyukan tsaro da tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

An shawarci al’ummar gari da su ci gaba da ba da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa ayyukan tsaro da tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *