Get the latest updates and insights on current events in the Sahel region. Sahel Reporters brings you breaking news and in-depth analysis.
Sports  

Musulmai Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Wa Gwamna Agbu Kefas

Daga Sani Yarima

Limamai da sauran Al’umman Musulmi sun gudanar da addu’o’i na musamman wa Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas, domin kara samun nasara wajen tafiyar da shugabanci da adalci a gwamnatin sa.

Anyi taron Addu’o’in ne a Masallacin Juma’ah dake unguwan Saurara a garin Jalingo wanda mai baiwa Gwamnan Shawara kan harkokin addinin musulunci,  Malam HussainiIsma’ila ya jagoran ta.

Manyan Limamai, Na’ibobi, Alarammomi, da daliban ilimi daga sassa daban-daban na Jihar Taraba, sune suka halarci Babban Masallacin Juma’ah dake Unguwar ta Saurara dake Jalingo inda suka fara da karatun Al’Qur’ani mai Tsarki.

Bayan kammala katun, sai akayi tawassali dashi wajen rokon Allah wa Gwamna Agbu Kefas, Jihar Taraba, Gwamnati da makarraban sa, dama Najeriya baki daya domin samun karin lafiya, zaman lafiya, kaunan juna, da bunkasan arziki mai albarka.

Manyan Malaman Addinin musulunci, da sauran al’umman Musulmi da suka halarci Masallacin sun kara jadda da goyon bayan su ga gwamnatin Agbu Kefas, inda suka suffanta shi da mutumin kirki mai Adalci.

Sun kuma roki Allah daya kara wa Gwamnan lafiya, hikima da basira, kana sun jinjina mishi kan kokarin da ya keyi na samar da ayyukan cigaba da bunkasa tattalin arzikin jihar.

Mai baiwa Gwamnan Shawara kan harkokin addinin Islama, Malam Hussaini Isma’ila wanda shine ya shirya taron Addu’o’in na musamman, yace babu abin da ya rage wa al’umman jihar Taraba illa kawai su yita godiya ga Ubangiji da yasa suka zabi Agbu Kefas a matsayin Gwamna, duba da irin ayyukan alkhairi da hada kan al’umman jihar daya tasa a gaba.

Malam Hussaini Isma’il, ya kuma kara rokon Musulmi maza da mata dasu zamo masu hadinkai, son zaman lafiya, tare da cigaba da baiwa gwamnatin Agbu Kefas goyon baya domin su kara samun romon dimukuradiyya kamar yadda ya gudanarwa.

Wannan Addu’o’in na musamman da Malam Hussaini Isma’il ya jagoran ta, ya nuna irin kyakkyawan halaka dake tsakanin al’umman Musulmi da gwamnatin Agbu Kefas a jihar ta Taraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *