Daga Sani Adamu Hassan
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da matakin bayar da tallafin N150,000 ga ƙanana da matsakaitan ƴankasuwar jihar Jigawa.
Mataimakin shugaban ƙasar ne Kashim Shetimma ya sanar da matakin yayin ƙaddamar da wani shiri na tallafawa ƙananan ƴankasuwa a Dutse babban birnin Jigawa a ranar Talata.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, mataimakin shugaban ƙasar ya ce za a bayar da tallafin ne ga kowane ɗankasuwar Jigawa kuma ba rance ba da ke buƙatar biya wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince.
Ya ce shiri ne na bunƙasa kasuwancin ƙananan ƴankasuwa a sassan jihohin Najeriya.
BBC Hausa ta rawaito cewa mataimakin shugaban Najeriyar ya kuma ƙaddamar da wasu ayyuka na bunƙasa harakar noma a Jigawa.