Hukumar yaki da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta tabbatar ta bullar cutar kyandir biri a jihohi 33 a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ta ce cutar bata kashe kowa ba, amma ta kama mutum 39.
Jihohin da ke kan gaba cikin masu cutar ta kyandir biri sun haɗa da Bayelsa (5), Cross River (5), Ogun (4), Lagos (4), Ondo (3), da Ebonyi (3).
A cewar shugaban hukumar ta NCDC Dr. Jide Idris, an sanya jihohin Legas, Enugu, Kano, Ribas, Cross-River, Akwa-Ibom, Adamawa, Taraba da kuma babban birnin tarayya Abuja cikin shirin ko-ta-kwana.
Wannan cuta dai tana ci gaba da yaɗuwa a kasashe da dama musamman kasashen Afrika, inda ta kashe mutum 450 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.
Cutar ta kyandir biri (mpox) tana cikin cututtukan da ke yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane. Tana kuma yaɗuwa ta hanyar mu’amala da me ɗauke da ita, sannan alamominta sun haɗa da mura da ɓarewar fatar jiki da ƙuraje.
Nasan likitoci da hukumomi za su dukufa wajen wayar da kan mutane kan wannan cuta. Don haka, yana da kyau mu ɗau shawarinsu domin tsira da lafiyarmu.