Daga Sani Yarima
An kara jawo hankalin Kiristoci dasu zamo masu riko da karantaswan Yesu Almasiyu tare da kaunan juna.
Babban Mai bushara na Majami’an Global Methodist Church dake Jalingo, Bishop John Pena Auta yayi wannan kiran a sakon sa na bikin kirsimeti.
Babban mai busharan na Majami’an Global Methodist Church (GMC) dake Jalingo, babban birnin jihar Taraba, Bishop John Pena Auta yace ta hanyan biyayya ga Ubangiji da kaunan juna ne kadai za’a sami jaman lafiya da salama a kasa baki daya.
Bishop ya kuma shawarci matasa dasu guji aikata alfalfa da shaye shaye.
Kazalika, Babban mai bukharan na Majami’an Global Methodist Church yayi kira ga masu rike da madafun iko dasu kasance masu rikon amanan al’umma.
Shima Shugaban Hukumar Tattara Kudaden Haraji na Jihar Taraba, Janar Jeremiah Faransa (Mai ritaya) wanda ya halarci Majami’an ta Global Methodist Church domin gudanar da addu’o’i, kira yayi ga ‘Yan Najeriya dasu kara hakuri da manufofin Gwamnati.
“Yace, duk da cewa manufofin suna da tsauri, toh amma idan aka daure, kowa zaiji dadi nan gaba kadan.”
Janar Jeremiah Faransa, ya kuma taya al’umman kirista munan bikin Kirsimeti tare dayin kira ga Musulmi da kirista su zauna lafiya da juna.
Wasu abokai mabiya addinin kirista, sun nuna farin cikin su na sake zagayowan ranar haihuwan Yesu Kiristi, suna masu ya kinin cewa shekara ta 2025 za tafi albarka.
Ande gudanar da shagul gulan lafiya aduk fadin kananan hukumomi goma sha shida dake jihar ta Taraba.