google.com, pub-7039602827030546, DIRECT, f08c47fec0942fa0
Connect with us

Hausa

Wasanni: UEFA Ta Dakatar Da Mourinho A Wasa 4 Kan Durawa Rafali Ashar

Published

on

Spread the love

Hukumar kula da kwallon kafar Turai ta bai wa kocin Roma, Jose Mourinho horon dakatarwa a wasanni 4 sakamakon tinkarar alkalin wasa dan kasar Ingila Anthony Taylor bayan da aka tashi daga wasan karshe na gasar Europa.

Ana zargin Mouronho mai shekaru 60 da tinkarar Taylor a wajen ajiyar motoci bayan an tashi wasan, inda ya duddura mai ashar.

Anthony Taylor ya bai wa dan kasar Portugal din katin gargadi a wasn karshe da Roma ta yi rashin nasara a hannun Sevilla a bugun daga- kai- sai- mai- tsaron -raga a wasan da suka fafata a Budapest.

Dukkannin kungiyoyin suna fuskantar tuhume-tuhume bisa irin tsagerancin da magoya baya da ‘yan wasansu suka nuna a yayin wasan.

An kuma haramta wa Roma sayar da tikiti ga magoya bayansu a wasa guda da za su fafata a waje a kaka mai zuwa, kana aka ci tara kungiyar kudi har fam miliyan 47 sakamakon yadda magoya bayansu ke ta jifa a cikin filin wasa a yayin wasa.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

TSADAN RAYUWA: A Dena Luwadi, Zina, Shan Giya, Chuta Da Zalunci- Ustaz Hamman Adama 

Published

on

By

Spread the love

Daga Sani Yarima 

An gargadi al’umman Musulmi dasu guji aikata luwadi, zina, shan giya, ha’inci, da duk sauran ayyukan sabon Allah.

Limamin Masallacin Juma’a na Muslim Council dake Jalingo, Ustaz Bashir Hamman Adama shine yayi gargadin a Huduban sa na Sallan Juma’a daya gudanar a yau 12/4/2024.

Ya karanto ayoyin Alqur’ani mai girma da Hadisan Manzon ALLAH (SAW) inda yace duk mai sabon Allah ya jira sakamako na zuwa, domin ba’a taba sabawa Allah a zauna lafiya kuma a gama da duniya lafiya, ba tare da an tuba ba. 

Hamman Adama ya lura da cewa, rashin gaskiya, cin amana, yaudara da ha’inci sunyi wa al’umma katutu a zamanin yanzu, adon haka yayi kira ga Musulmi dasu gyara ayyukan su, su tuba su koma ga Allah.

Ya kara jaddada bukatar Dake akwai na “Jama’a su guji son duniya fiye da jin tsoron Allah, su dena shan giya, zina, karya, da dukkan sauran ayyukan fasikanci a doron kasa domin samun tsira ranan gobe kiyama.

“A fifita jin tsoron Allah fiye da wani shugaba ko mai arziki. Kawai za kaga mutane sunfi jin tsoron Gwamna, ko wani Dan Majalisa, ko Mai kudi fiye da maganan Allah. Tohh wallahi mu tuba mu koma ga Allah.

“A lokacin watan Ramadan daya gabata, Malamai sun fassara ayoyin Alqur’ani a ko ina, toh amma saboda sakaci al’umma da damana basu daukan darasin sabo da son duniya.

“Rashin tawakkali da tsoron Allah shi yasa Jama’a ke cikin wahala,” inji Ustaz Hamman Adama.

Ya kuma yi kira ga masu hanu da shuni dasu rinka ciyar da marasa galihu, marasa lafiya, Marayu, gyara Masallatai, yana mai cewa bawai lalle sai masu kudi ba, idan har Mutum nada koda naira dari (N100) ne, toh zai iya taimakawa wani ko masallaci da nera hamsin.

A wata ayar Al’qur’ani Mai Girma daya jawo “ALLAH (SWA) ya bayyana masu aikata wadannan abubuwan alkharin da cewa sune mumunai na gaskiya Kuma ALLAH yayi alkawarin yin gafara gare su a ranan kiyama.

Malamin addinin Musuluncin, Ustaz Bashir Hamman Adama ya kara jaddada bukatar dake akwai na al’umman Musulmi dasu tuba zuwa ga Ubangiji, domin acewar sa alamun ‘”Tashin Alkiyama yazo”.

Continue Reading

Hausa

Labarun Wasu Jihohin Najeriya Dana Kasar Waje 

Published

on

By

Spread the love

By Sani Yarima

Dukufa Kan Noma Cikin Gaskiya Shi Zai Wadatar Da Abinci A Najeriya – Inji Raymond Enoch 

Mai kamfen din bunkasa lamuran noma karkashin majalisar dinkin duniya a Najeriya, Raymond Enoch ya ce dukufa kan noma da gaske ne zai taimaka wajen wadatar da abinci a Najeriya.

Raymond Enoch wanda ke jagorantar shirin bunkasa noma a tsakanin iyalai ya ce ‘yan filayen da a ke nomawa hantsi biyu ko uku ba za su samar da abun da akasarin iyalai ke bukata na abinci ba.

Kazalika ya ce su kuma manyan manoma na yin noman don kasuwanci inda ‘yan baranda ke sa hannu wajen tsadar abinci.

A nan Enoch ya ce akwai bukatar rungumar noman zamani ko da kuwa da amfani ne da takin gargajiya.

Masanin ya ba da shawarar zuba jarin gwamnati a harkar noma da kuma kawar da duk harajin da ke shafar manoma.

JIHAR ZAMFARA TA KAFA DOKAR HANA RATSA JIHAR DAGA KARFE BAKWAI NA YAMMA ZUWA KARFE SHIDA NA SAFE (7PM-6AM). 

Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa dokar hana ratsa jihar daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe daga kan iyakar ta da Katsina da kuma Sokoto.

Kwamishinan labaru na jihar, Mannir Mu’azu Haidara ya baiyana hakan a Gusau.

Matakin dai inji gwamnatin don dakile ta’addancin barayin daji ne.

Gwamnatin ta ba da shawarar masu tafiye – tafiye su ba da hadin kai ga wannan doka don amfaninsu ne.

Labarin dai bai fadi iya tsawon wa’adin dakatar da zirga-zirgar ba.

GWAMNATIN JIHAR TARABA TA WARE NAIRA BILIYAN DAYA (N1bn) DOMIN BIYAN MA’AIKATAN DA SUKA YI MURABUS

Gwamnan Jihar Taraba, Dakta Agbu Kefas ya bada umurnin gaggauta biyan ma’aikatan gwamnati da suka Yi ritaya a jihar hakkokin su na giratuti inda ya amince da a cire naira biliyan daya bayan kwashe shekaru kusan goma sha uku da rashin biyan.

Gwamnan ya kuma amince da a rinka cire naira miliyan dari biyu (N200m) a ko wane wata domin samun daman cigaba da biyan ma’aikatan kudin na giratuti.

A JIHAR KADUNA KUWA, GWAMNA UBA SANI YA KOKA BISA IRIN BASHIN DA YACE TSOHON GWAMNAN JIHAR, NARISU EL-RUFA’I YA CIWO DA KUMA AYYUKAN DA BA’A KAMMALA SU BA ANBAR SU

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya fito ya shaida WA duniya cewa shiga da alama bazai iya biyan albashin ma’aikatan gwamnati ba bisa zargin cewa wanda ya gada, Nasiru El-rufa’i yayi wa jihar gammo da bashi tare da barin ayyuka masu yawa wanda ba’a kammala su ba.

A cewar Uba Sani, ya gaji bashin dalan Amuruka miliyan tamanin da bakwai ($587m) da naira biliyan tamanin da biyar (N85bn) a kudin gida Najeriya daga tsohon Gwamna, Nasiru El-rufa’i. 

AN SACE DALIBAN JAMI’AR GWAMNATIN TARAYYA DAKE WUKARI NA JIHAR TARABA

A ranar Litinin, 1 Apirilu 2024 ne aka yo garkuwa da wasu dalibai guda biyu a Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake karamar hukumar wukari a jihar Taraba.

Babban Jami’in tsaro na Jami’ar, Sule Gani ya shedawa manema labarai cewa daliban anyi garkuwa dasu ne da yammaci a wani dakin saida abinci dake cikin Jami’ar, toh Amma yace dasu da sauran Jami’an tsaro sun bazama domin ceto daliban cikin koshin lafiya.

Ya zuwa yanzu de babu wani sako daga wadan da suka yi garkuwa da daliban Kona neman kudin fansa ko kuma wani Abu daban. 

KASAR TAIWAN TA FUSKANCI GIRGIZAN KASA

A ranar Laraba 3, Apirilu, 2024, mummunan girgizan kasa mai nauyin 7.4 ya faru a kasar Taiwan inda yayi sanadiyan mutuwan mutane hudu (4) tare da rusa gine gine masu yawa a garin Hualien.

Kkafar sadarwa ta BBC, ta ruwaito cewa Jami’ai masu ceto suna cigaba da kai dauki don ceto mutane.

A cewar kafar ta BBC, a watan Satumba na shekara 1999 wani girgizan kasan mai girman 7.6 ya afku a Kasar ta Taiwan inda yayi sanadiyan mutuwan mutane dubu biyu da dari hudu (2,400) tare da rusa gine gine dubu biyar (5000).

Continue Reading

Hausa

Matashi Ya Canja Sunan Ƴarsa Zuwa Na Mahaifiyar Shugaba Tinubu Saboda Soyayya

Published

on

By

Spread the love

Wani matashi mai matsakaicin shekaru a jihar Bauchi, Khamees Darazo, wanda ya kasa boye soyayyar sa ga shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Asabar din da ta gabata ya cika alkawarin da ya dauka lokacin da ya fito fili a hukumance ya canza sunan diyarsa ta farko mai shekaru 2, Hauwa zuwa Abibatu sunan Mahaifiyar Bola Tinubu.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata walima na musamman da ya shirya tare da abokansa, wanda aka gudanar a dakin taro na Double 4 da ke cikin garin Bauchi, inda ya bayyana cewa matakin shi ne hanyarsa na nuna goyon baya da biyayya ga Shugaba Bola Tinubu.

A cewarsa, “Bayyana goyon bayana ga Shugaban kasa ya faro ne a lokacin da na sadaukar da dukkan alawus din NYSC ɗina, a lokacin da na hidimta wa ƙasa a Jihar Gombe, domin karfafa yunkurin yakin neman zaben Shugaban kasa a tunkarar zaben Shugaban kasa na shekarar 2023.

Wani fata zaku yi wa Malam Khamees da ‘yarsa Abibatu mai sunan Mama?

Continue Reading

Trending

Copyright © 2021 Sahel Reporters